Bishiyar Annabci ta fara fitar da 'ya'yanta, yayin da Fatima ta haifi Hasan sannan Husaini. Tarihi dai ya tabbatar da cewar Manzon Allah (s.a.w.a) ya tarbi wadannan jarirai da irin tarbar da ya yiwa haihuwar Fatima, inda ya sa musu suna Hasan da Husaini. Hakika sun sami matsayi irin na uba mai tausayi ga 'ya'yansa a zuciyar Manzo. Wannan alaka ta ubantakar ruhi tsakanin Manzon Allah (s.a.w.a) da Hasan da Husaini ta fara tun daga ranar haihuwarsu, wato alakar Annabci da Imamanci.
An ruwaito shi (s.a.w.a), alhali yana rungume da 'ya'yan Fatima, Hasan da Husaini, yana cewa:
"Duk wani da ga wani uba, tsatsonsa na fitowa ne (kai tsaye) daga ubansa in ban da 'ya'yan Fatima; domin lallai ni ne ubansu kuma tsatsonsu(1)".
"Wadannan 'ya'yana ne, wanda ya so su, to hakika ya so ni (2)".
"Hasan da Husaini shugabannin matasan Aljanna ne(3)".
"Hasan da Husaini Imamai ne sun yunkura (don haka) ko ba su yunkura ba".
"Wanda ya so Hasan da Husaini hakika ya so ni, wanda ya fusata su kuma ya fusata ni (4)".
Wadannan zantuka na Manzon Allah (s.a.w.a) da ke nuna kaunarsa ga wannan tsarkakkan gida ba su samo asali daga alakar iyalantaka ba; domin shi Manzon Allah ne da ba ya zance bisa son zuciya, shi ne wanda Allah Madauakaki Ya yi horon da yin koyi da shi; kenan ba ya kauna ko ki face don Allah kawai.
Zantukansa kan Ahlulbaiti (a.s.) ba su kasance ba face bayanin daukakar darajarsu a wajen Allah Madaukaki, da fayyace matsayi da aikinsu a cikin wannan al'umma, ta yadda har Manzo (s.a.w.a) ya ke fadi wa Ali, Fatima, Hasan da Husaini (a.s.) cewa:
"Ni mai yaki ne da wanda ya yake ku, kuma mai zaman lafiya da wanda ya zauna lafiya da ku"(5).
Bayan Hasan da Husaini, Fatima (a.s.) ta haifi Zainab al-Kubrah, gwarzuwar Karbala, kuma abokiyar tarayyar Husaini (a.s.) a jihadi da gwarzantakarsa. Haihuwarta ta kasance a ranar sha bakwai ga watan Rajab, shekara ta biyar bayan hijira. Sai aka isar da albishir zuwa ga Manzo (s.a.w.a), shi kuma sai ya fuskanci gidan 'yarsa Fatima yana mai taya ta murna da farin ciki; sannan ya sa wa abin haihuwa suna Zainab.
Sannan Fatima ta haifi wata 'yar, wadda ta kasance ta hudu daga 'ya'yan Fatima. Da labarin ya isa wajen Manzo (s.a.w.a) sai ya zo, kamar yadda ya saba, gidanta ya taya ta murna, sannan ya sa wa abin haihuwa suna Zainab al-Sugrah, daga baya aka yi mata lakabi da Ummu Kulthum.
____________
1- Dabari, cikin Zakha'irul-Ukbah, shafi na 121
2- Dabari, cikin Zakha'irul-Ukbah, shafi na 124.
3- Ahmad, Tirmizi da Ibn Majah sun fitar da shi.
4- Sahihu Ibn Majah, babin darajojin Hasan da Husaini (a.s.).
5-Hakim ya ruwaito shi a cikin al-Mustadrik, juzu'i na 3, shafi na 149, da Ibn Majah a gabatarwar Sunan din shi, juzu'i na 1, shafi na 52; da Ahmad bin Hambali cikin Musnad, juzu'i na 2, shafi na 442; da wasun wadannan.